Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bukaci Amurka ta nazarci kanta da kanta don gyara kuskurenta
2020-07-18 16:20:45        cri

Kasar Sin tare da wasu kasashe da dama, sun bayyana ra'ayinsu dangane da batun kare hakkin dan Adam a Amurka, suna masu bukatar Amurkar ta tunkari matsalolinta tare da inganta kare hakkin bil adama.

Kasashen sun bayyana haka ne, yayin taro na 44 na hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD da aka yi a Geneva.

Yayin da ake tattaunawa kan nau'ikan wariyar launin fata, kasar Sin ta gabatar da wata sanarwar hadin gwiwa a madadin ayarin wasu kasashe, inda suka bayyana cewa, shekaru 20 bayan cimma yarjejeniyar birnin Durban ta yaki da wariyar launin fata, har yanzu lamura irin na kisan George Floyd na ci gaba da faruwa, kana rukunoni masu rauni na mutuwa sakamakon wariyar launin fata da cin zarafi daga 'yan sanda, wadanda ke nuna yadda wadannan matsaloli da gibin dake tsakannin al'umma suka yi kaka-gida a Amurka.

Har ila yau, kasar Sin ta bayyana adawa mai karfi da dukkan nau'ikan wariyar launin fata. Inda ta ce ta damu da wariya da tsangwamar da wasu 'yan siyasa ke nunawa a wasu kasashe yayin da ake fama da cutar COVID-19.

Da ake tattaunawa kan batun sauyin yanayi da hadin gwiwar kasa da kasa kuwa, kasar Sin ta ce yayin da ake tsaka da fuskantar sauyin yanayi a duniya, Amurka, a matsayinta na kasa ta biyu mafi fitar da sinadarin Carbon, ta janye daga yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris. Tana mai cewa, yin gaban kai irin haka, na illata kuduri da yakinin kasashen duniya na hada hannu wajen magance sauyin yanayi, da kuma illata hakkokin al'ummun dukkan kasashe.

Dangane da batutuwan wasu kasashe kuma, Sin ta bayyana damuwa kan takunkuman da Amurka ta kakabawa Sudan da Syria da Venezuela, tana mai jaddada cewa, takunkuman suna mummunan tasiri kan ci gaban tattalin arziki da zaman takewar wadancan kasashe, lamarin dake jefa jama'arsu cikin mawuyacin hali da yi wa kokarinsu na yaki da COVID-19 cikas. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China