Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ce kan gaba wajen keta hakkin bil Adama, in ji ma'aikatar wajen Sin
2020-07-16 21:01:18        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Sin Hua Chunying, ta ce kasar Amurka ce kan gaba a duniya, wajen keta hakkin bil Adama.

Kalaman Hua na zuwa ne bayan, da sakataren wajen Amurka Mike Pompeo ya sanar da cewa, kasar sa za ta kakaba takunkumin hana VISAr shiga Amurka, ga ma'aikatan wasu kamfanonin fasahar kasar Sin, ciki hadda na kamfanin Huawei, saboda zargin cewa wai kamfanonin na Sin, na keta hakkokin bil Adama.

Game da hakan, jami'ar ta ce "duk da cewa Amurka na yawan yayata batun kare hakkin bil Adama, amma a bayyane take cewa, ita ce ke kan gaba a duniya wajen keta hakkokin bil Adama. Ta ce zargin da Amurka ke yi cewa Sin na keta hakkokin bil Adama a jihar Xinjiang, karya ce tsagwaron ta, kuma ya kamata Amurka ta ji kunyar yadda manyan jami'an ta ke sharara karya, game da wannan batu.

Hua Chunying ta kara da cewa, kamata ya yi Sinawa su bayyanawa duniya, ko ana kare hakkokin su ko a'a, maimakon jin hakan daga 'yan siyasar Amurka. Ta ce a kasar Sin akwai kabilu daban daban har 56, dake zaune cikin lumana da juna, kuma daukacin al'ummar kasar biliyan 1.4 na rayuwa da aiki, da cudanya cikin kyakkyawan yanayi da gamsuwa.

Bugu da kari, cikin shekaru sama da 40 da suka gabata, kudaden shigar al'ummar Sinawa ya karu da sama da rubi 25. An kuma tsamo al'ummun kasar sama da miliyan 850 daga kangin talauci, yayin da gudummawar kasar a fannin rage fatara a duniya ta haura kaso 70 bisa dari. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China