Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Dage zaben yankin Hong Kong shawara ce mai kyau
2020-08-03 19:57:41        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana cewa, dage zaben 'yan majalisar dokokin yankin musamman na Hong Kong da aka yi, shawara ce mai kyau wadda kuma ta zama tilas.

Wang wanda ya bayyana haka, yayin taron manema labaran Litinin din nan, ya ce dage zaben, shawara ce da ta zama tilas, don kare lafiyar jama'a, tare da tabbatar da cewa, an gudanar da zaben bisa adalci ba tare da wata rufa-rufa ba.

Ya ce, zaben 'yan majalisar dokokin yankin, zabe ne da ya shafi kasar Sin, don haka, batu ne na harkokin cikin gidan kasar Sin.

A ranar 31 g watan Yuli ne, jagorarar yankin musamman na Hong Kong, Carrie Lam ta sanar da dage zaben, wanda a baya aka shirya gudanarwa a ranar 6 ga watan Satumba, saboda annobar COVID-19.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China