Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar lafiyar Sin za ta tura tawagar binciken kwayar cutar COVID-19 zuwa HK
2020-08-02 17:08:32        cri

A cikin 'yan kwanakin baya bayan nan, yankin musamman Hong Kong na kasar Sin ya shiga yanayi mai tsanani yayin da yake kokarin dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19, don haka hukumar lafiya ta kasar Sin za ta tura tawagar masu binciken kwayar cutar zuwa yankin bisa bukatar da gwamnatin yankin ta gabatar wa gwamnatin tsakiyar kasar, domin samar da tallafi ga yankin a bangaren yaki da annobar.

Tawagar binciken ta farko da za a tura za ta fito ne daga lardin Guangdong, wadda za ta kumshi ma'aikatan jinya guda 60 da suka zo daga asibitoci 20 a fadin lardin, a ciki, guda bakwai za su tashi zuwa yankin Hong Kong a ranar 2 ga wata.

A sa'i daya kuma, hukumar lafiya ta kasar Sin ta riga ta zabi ma'aikatan jinya kimanin 6 daga birnin Wuhan na lardin Hubei wadanda ke da kwarewa kan aikin jinya dake cikin asibitocin wucin gadi, domin samar da tallafin fasaha ga asibitin wucin gadin da aka kafa a cibiyar baje kolin kasa da kasa na Asiya na Hong Kong.

Alkaluman da hukumar lafiya ta yankin Hong Kong ta fitar sun nuna cewa, a ranar 31 ga watan Yulin da ya gabata, adadin sabbin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a yankin ya kai 125, a cikinsu, mutane 124 sun kamu da cutar ne a yankin, gaba daya adadin masu cutar a yankin ya kai 3397.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China