Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Margaret Chan: Dage zaben majalisar dokokin HK zai taimaka wajen kare lafiyar jama'a
2020-08-02 16:21:24        cri

Matakin da aka dauka na dage zaben 'yan majalisar dokokin yankin musamman na Hong Kong HKSAR, na shekarar 2020 ya zo a daidai lolacin da ya dace domin kare lafiyar al'umma mazauna yankin na Hong Kong, tsohuwar babbar daraktar hukumar lafiya ta duniya WHO, Margaret Chan, ta bayyana hakan.

Ta ce a matsayinta na tsohuwar babbar daraktar hukumar WHO kuma mambar al'ummar yankin Hong Kong, tana cikakken goyon bayan matakin da gwamnatin HK ta dauka na dage zaben 'yan majalisar dokokin yankin, mataki ne da ya zo a daidai lokacin da ya dace, da farko an tsara yin zaben ne a ranar 6 ga watan Satumbar 2020, matakin zai kare lafiya da zaman rayuwar al'ummar yankin Hong Kong.

Margaret Chen ta ce, hakika, sama da kasashen duniya 60 sun dage zabukansu domin rage barazanar yaduwar annobar COVID-19 wacce ke ci gaba da ta'azzara a duniya. Ta bayyana hakan ne cikin wani sharfi da aka wallafa a jarida.

Haka zalika ta yabawa gwamnatin yankin musamman na HK bisa matakin da ta dauka na neman taimako daga babban yankin kasar Sin domin kara inganta fannin kiwon lafiyar yankin don samar da kayayyakin gwaje gwajen kwayar cutar COVID-19 da samar da karin gadaje a cibiyoyin killace masu fama da cutar, kana tsohuwar shugabar hukumar WHO ta kara jaddada muhimmancin yin hadin gwiwa wajen yaki da annobar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China