Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Birtaniya ya soki yunkurin kasashen yamma na kawo cikas ga dokar tsaron kasar Sin kan HK
2020-07-06 10:52:43        cri

Shahararren masanin kasar Birtaniya, Martin Jacques, na ta wallafa bayanai a shafin sada zumunta a kai-a kai, inda ya ke sukar yunkurin kasashen yamma na kawo cikas ga dokar tsaron kasar Sin kan yankin Hong Kong.

Martin Jacques, ya ce, bisa la'akari da yanayin da HK ke ciki, shin kasar Sin ta na da wani zabi ne da ya wuce zartar da dokar tsaro a yankin? Shin akwai wata kasa a yammacin duniya da za ta bari a shafe watanni ana rikici a manyan biranenta? Ya ce gaskiyar magana ita ce, kasashen yamma za su dauki irin matakin da Sin ta dauka. Ya ce dole ne kasashen yamma su dauki alhakin rikicin a HK, saboda goyon bayansu na daya daga cikin muhimman abubuwan da suka haifar da rikicin.

Masanin ya kara da cewa, "kasa daya mai tsarin mulki 2" ta kasance muhimmiyar manufa mai ma'ana. Kuma tunanin kasar Sin, ba daya yake da na Birtaniya ba. Har ila yau, ya ce Birtaniya da ta kasa amincewa da sauyin lokacin mulkin mallaka, na son daukar HK a matsayin wadda ke karkashin yammacin duniya, bayan ainihin batu shi ne, HK mallakar kasar Sin ne. Ya ce a bayyane yake yanzu cewa, ba goyon baya kadai masu tada rikici a yankin ke samu daga kasashen yamma ba, har ma da tallafin kudi daga Amurka.

Yayin taron hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD a Geneva, kasashe mahalarta 53 sun goyi bayan sabuwar dokar kasar Sin a kan HK, yayin da 27 suka nuna adawa da ita. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China