Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar harkokin wajen Sin ta yi tsokaci game da zartar da dokar tsaron kasa a HK
2020-07-01 10:21:24        cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta yi tsokaci, bayan zartar da dokar tsaron kasa a yankin musammam na Hong Kong, yayin zama na 20 na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin.

Kakakin ma'aikatar ya ce, zaunannen kwamitin ne ya tsara dokar, kuma ya sanya ta cikin daftarin dokokin yankin musammam na HK, wadda gwamnatin yankin za ta wallafa tare da zartarwa, yana mai cewa wannan, ita ce mafita wajen dawo da zaman lafiya da kawo karshen rikici a HK.

Ya ce dokar ta shafi rukunonin laifuffuka 4 dake tarnaki ga tsaron kasa. Yana mai cewa za ta mai da hankali ne kan tsirarun masu aikata laifuffuka, sannan ta kare galibin al'ummar yankin.

Ya kara da cewa, aiwatar da ita, zai karfafa tsarin shari'a a HK da tabbatar da zaman lafiya da inganta muhallin kasuwanci, sannan za ta amfanawa mazauna yankin da baki masu zuba jari. Yana mai cewa, suna da yakini game da makoma mai haske a HK.

Bugu da kari, kakakin ya ce, HK daya ne daga cikin yankunan Sin na musammam, kuma batutuwan da suka shafe ta, batutuwa ne na cikin gida. Gwamnatin kasar Sin ta himmantu wajen aiwatar da manufar "kasa daya mai tsarin mulki biyu", kuma tana adawa da tsoma baki cikin harkokin HK. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China