Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na adawa da matakin Amurka na takaita ba da bisa ga jami'anta saboda batun HK
2020-06-27 16:35:12        cri

Ofishin jakadancin kasar Sin dake Amurka, ya bayyana a jiya cewa, Sin na adawa da matakin Amurka na takaita ba da bisa ga jami'an kasar saboda batun Hong Kong, tana mai kira ga Washington da ta daina tsoma baki cikin harkokinta na cikin gidan.

Sanarwar da ofishin jakadancin ya fitar, ta ce HK wani bangare ne na kasar Sin, kuma batutuwan da suka shafi yankin, batutuwa ne na cikin gidan kasar Sin da ba sa bukatar a yi musu katsalandan.

Ta kara da cewa, zartar da dokar tsaron kasa iko ne da hakkin gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, sannan batu ne na cikin gida. Tana mai cewa dokar tsaron kasa kan HK na mayar da hankali ne kan wasu ayyuka kalilan da ka iya illata tsaron kasar.

A cewar sanarwar, dokar za ta inganta tsarin shari'a a HK, lamarin da zai kai ga samun kwanciyar hankali da ba da gudunmuwa wajen aiwatar da manufar "kasa daya mai tsarin mulki biyu" da samar da ci gaba mai dorewa a yankin.

Bugu da kari, sanarwar ta yi kira ga Amurka, da ta gyara kuskurenta, ta janye matakin, tare da daina tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin. Tana mai cewa, kasar Sin za ta ci gaba da daukar matakai masu karfi na kare cikakken 'yanci da tsaro da kuma muradunta na ci gaba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China