Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Naurar binciken duniyar Mars ta Sin ta kammala zagayen farko na gyaran hanyar kewaya
2020-08-02 15:29:44        cri

Na'urar binciken duniyar Mars ta kasar Sin, samfurin Tianwen-1, ta yi nasarar kammala aikin gyaran hanyar kewaya na farko da safiyar yau Lahadi, hukumar kula da ayyukan sararin samaniyar kasar Sin CNSA ta sanar da hakan.

Na'urar ta kammala aikin ne da misalin karfe 7 na safe agogon Beijing, bayan injin na'urar samfurin 3000N ya gudanar da aiki cikin dakikoki 20, daga bisani ta kama hanyar zuwa duniyar Mars. Dukkan tsarin na'urar yana cikin yanayi mai kyau.

Kafin gudanar da aikin gyaran hanyar kewaya, na'urar aikin binciken ta yi tafiyar sama da sa'o'i 230 a sararin samaniya, kuma adadin tafiyar ya kai nisan kilomita miliyan 3 daga duniyarmu.

Shirin ya kuma gwada lafiyar injin samfurin 3000N. Nan gaba na'urar za ta gudanar da wasu ayyukan gyare gyare masu yawa a cikin tafiyar zuwar duniyar Mars na wa'adin sama da watanni shida, kamar yadda majiyar hukumar CNSA ta bayyana.

Kasar Sin ta harba na'urar binciken duniyar Mars a ranar 23 ga watan Yuli, wanda aka tsara domin gudanar da ayyukan binciken sararin samaniya, wannan shi ne matakin farko na aikin bincike a duniyar rana. Ana sa ran na'urar binciken za ta iya kaiwa duniyar Mars nan da watan Fabrairun shekarar 2021.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China