Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi nasarar harba na'urar binciken duniyar Mars
2020-07-23 15:22:38        cri

Da karfe 1 saura mintuna 19 na tsakar ranar yau Alhamis bisa agogon Beijing ne, aka cimma nasarar harbar rokar Changzheng-5, dake dauke da na'urar binciken duniyar Mars mai suna Tianwen-1 da kasar Sin ta kera, kuma irin ta ta farko zuwa sararin samaniya, daga filin harbar taurarin dan Adam na Wenchang dake tsibirin Hainan na kasar Sin.

Ana fatan dai na'urar za ta yi kewaye, da sauka, ta kuma yi tafiya a doron duniyar Mars, za kuma ta gudamar da matakin farko na bincike kan duniyar rana.

A cewar hukumar lura da sufurin sama jannati ta kasar Sin ko CNSA a takaice, rokar Long March-5 mafi girma da kasar ke amfani da ita wajen dakon kumbuna, dauke da nauyin kusan tan 5, ta keta sararin samaniya, kuma bayan mintuna kusan 36 ta kai tashar musayar falaki tsakanin duniyar mu da duniyar Mars, inda daga nan ne kuma rokar ta fara tafiyar kusan watanni 7 zuwa Mars.

An radawa shirin farko na kasar Sin na zuwa duniyar Mars sunan Tianwen-1, wanda ke nufin "Tambayar sararin samaniya". Sunan ya kuma samo asali ne daga wata dadaddiyar wakar gargajiya da wani mawaki mai suna Qu Yuan, wadda ya rera a shekarun kusan 340-278 kafin haihuwar Isa Almasihu, wakar da ta kasance daya daga mafiya shahara a tarihin wakokin gargajiya na da, a nan kasar Sin.

Sunan na nuni ga irin nacewa da kasar Sin ke yi wajen binciko gaskiya, da zurfafa binciken kimiyya, da gano abubuwan dake kunshe cikin asalin rayuwa, da duniyar bil Adama, kamar dai yadda hukumar ta CNSA ta bayyana.

Geng Yan, jami'i ne a hukumar lura da binciken duniyar wata, da cibiyar shirin kasar Sin na sufurin sama jannati, ya kuma bayyana cewa, nasarar harba wannan na'ura, matakin farko ne na burin Sin game da binciken duniyar Mars, kuma kasar na fatan dukkanin muhimman matakai na gaba, cikin wannan doguwar tafiya za su kammala cikin nasara.

Ya kara da cewa, muhimman matakan da ake fatan aiwatarwa sun hada da na rage saurin rokar yayin da ta kusanci duniyar Mars, da sarrafa yanayin kewayen ta, da rabuwar sashen sauka da na'urar binciken daga na'urar da ke taimakawa kewayen ta, har ta kai ga sauka cikin sauki, ta kuma yi tattaki bisa tsari a doron duniyar ta Mars. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China