Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Na'urar binciken duniyar Mars ta Sin ta dauki hotunan duniyarmu da duniyar wata
2020-07-29 11:49:58        cri

Na'urar binciken duniyar Mars ta kasar Sin, samfurin Tianwen-1, ta dauki hotuna a duniyarmu da duniyar wata, daga nisan kusan kilomita miliyan 1.2 daga duniyarmu, hukumar kula da ayyukan sararin samaniyar kasar Sin CNSA ta sanar da hakan a ranar Talata.

Kasar Sin ta harba na'urar binciken duniyar Mars, samfurin Tianwen-1, a ranar 23 ga watan Yuli, wannan shi ne matakin farko na aikin bincike a duniyar rana.

A cewar hukumar ta CNSA, na'urar ta yi nasarar haye giragizan sararin samaniya, kana ta yi tafiyar sama da kilomita miliyan 1.5 daga duniyarmu.

Na'urar binciken tana cikin yanayi mai kyau, kamar yadda hukumar CNSA ta bayyana.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China