Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na daf da harba tauraron dan-Adam na Tianwen-1 zuwa duniyar Mars
2020-07-17 10:26:56        cri
Hukumar kula da zirga-zirgar sararin samaniya ta kasar Sin, ta bayyana cewa, yanzu haka na'urar bincike din ta mai suna Tianwe-1 da kasar ke shirin harbawa zuwa duniyar Mars, ta isa cibiyar harba taurarin dan-Adam ta Wenchang dake tsibirin Hainan na kudancin kasar, kuma dukkan shirye-shiryen sun yi nisa yadda ya kamata.

Bayanai na nuna cewa, a cikin ko wadanne watanni 26, duniyar Mars na kara kusanto duniyarmu a cikin falakinta, kuma shi ne lokacin da ya dace kuma mafi kusa na harba na'urar, kana lokacin ne da na'urar ba ta bukatar mai mai yawa.

A watan Afrilu ne dai, kasar Sin ta sanar da cewa, Tianwen-1, shi ne sunan na'urar bincike ta farko da za ta harba duniyar ta Mars. Kamar yadda aka tsara, kasar Sin tana shirin harba na'urar da za ta rika kewaya falaki, sauka kan duniyar ta Mars.

Za dai a yi amfani da rokar Long March-5 wajen harba na'urar ta Tianwen-1.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China