Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Alkaluman PMI na kasar Sin ya karu zuwa 51.1 a watan Yuli
2020-07-31 13:27:44        cri
Hukumar kididdiga ta kasar Sin(NBS) ta sanar a Jumma'ar nan cewa, alkaluman dake nuna karfin tattalin arziki a bangaren masana'antun kasar, sun karu daga 50.9 na watan Yuni zuwa 51.1 a watanYuli.

Sama da 50 na alkaluman dai, na nuna alamu na karuwa, yayin da kasa da haka ke nuna raguwa. Watanni biyar ke nan a jere, alkaluma ke ci gaba da karuwa.

Da yake Karin haske kan dorewar wannan karuwa, babban jami'i a hukumar NBS Zhao Qinghe, ya ce, manufofin da kasar ta bullo da su game da kandagarkin annoba da raya tattalin arziki, sun kara haifar da kyakkayawan sakamako, a yayin da tattalin arzikin kasar ke ci gaba da farfadowa, a hannu guda kuma masana'antu ke kara gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China