Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rufe karamin ofishin jakadancin Amurka dake Chengdu ya dace da doka, in ji ma'aikatar harkokin wajen Sin
2020-07-27 19:24:15        cri
Mai Magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce umarnin da kasar Sin ta bayar na rufe karamin ofishin jakadancin Amurka dake birnin Chengdu tare da amshe iko da shi ya dace da dokar kasa da kasa, da ma yanayin cudanyar kasa da kasa.

Da yake tsokaci game da rufe ofishin, yayin taron manema labarai da gudanar a Litinin din nan, Mr. Wang ya ce matakin na Sin, ya biyo bayan rufe karamin ofishin jakadancin Sin dake birnin Houston ne da mahukuntan Amurka suka yi, tare da kutse da jami'an na Amurka suka yi cikin ginin ofishin.

Jami'in ya ce, Sin ba ta jin dadin yanayin da dangantakar ta da Amurka ta shiga ba. To sai dai kuma a cewar sa, Amurka ce ke da alhakin yanayin da aka shiga.

Daga nan sai ya yi kira ga mahukuntan Amurka, da su gaggauta gyara kurakuran da suka tafka, su kuma samar da kyakkyawan yanayin sake komawa kan tsarin dangantaka mai armashi tsakanin kasashen biyu, domin samar da ci gaba kamar yadda aka saba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China