Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta mai da martani ga matakin rashin imani da Amurka ta dauka
2020-07-29 10:20:46        cri

Jiya Talata, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya zanta da takwaransa na kasar Faransa Jean-Yves Le Drian ta wayar tarho, inda ya bayyana ra'ayinsa game da dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka.

Wang ya ce, a halin yanzu, kasashen duniya na damuwa kan dangantakar Sin da Amurka, saboda wasu 'yan siyasar Amurka sun yi biris da tarihin dangantakar kasashen biyu, inda suka dauki matakan da ba su dace ba na matsawa kasar Sin lamba ta hanyar takalar muhimman muradun kasar Sin bisa dalilai na siyasance don kawai neman zabe.

A cewar Wang Yi, Sin za ta mai da martani yadda ya kamata.

Da farko, Sin za ta dauki mataki don mai da martani ga matakan da Amurka ta dauka da suke keta muradun kasar Sin.

Na biyu, kamata ya yi kasashen biyu su yi shawarwari yadda ya kamata. Sin tana fatan Amurka za ta yi la'akari da muradun jama'ar kasashen biyu da ma na duniya baki daya, don ba da tabbaci ga dangantakar kasashen biyu ta hanyar sulhuntawa.

Na uku, kamata ya yi kasashen duniya sun yi iyakacin kokarin kiyaye hadin kansu.

Wang Yi ya kara da cewa, yana da imani cewa, duniya na da makoma mai haske, saboda zaman lafiya da hadin kai ita ce hanya mafi dacewa da duk bil Adama za su bi, babu wata kasa da za ta iya kaucewa wannan mataki kuma duk yunkurin kawo cikas ga wannan mataki ba zai yi nasara ba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China