2020-07-29 10:30:56 cri |
A halin yanzu, ana kokarin canja tsarin raya masana'antun samar da kayayyaki na birnin Shanghai. A watan Yuni na bana, an gabatar da shirin ayyukan shekaru 3 wato daga shekarar 2020 zuwa 2022 a birnin Shanghai, inda aka tsara da cewa, ya zuwa shekarar 2022, yawan kudin da za a samu daga manyan masana'antu ta yanar gizo a birnin zai karu daga Yuan biliyan 80 zuwa biliyan 150, ta yadda zai sanya birnin Shanghai zama wuri mafi samun albarkatun tsarin raya masana'antu ta yanar gizo, da yin kirkire-kirkire, da raya sana'o'i, da kuma bude kofa ga kasashen waje da yin hadin gwiwa a fadin kasar Sin.
Shugaban hukumar raya tattalin arziki da sadarwa ta birnin Shanghai Wu Jincheng ya yi bayani cewa, a halin yanzu, an riga an sa kaimi ga raya kamfanoni fiye da 300 wajen inganta masana'antunsu ta yanar gizo a fannonin fasahohin wutar lantarki, magunguna, motoci, karafa, binciken sararin samaniya da sauransu, kana an jawo kamfanoni kanana da matsakaita dubu 100 zuwa dandalin raya su ta yanar gizo. A shekaru 3 masu zuwa, za a gina kamfanonin samar da kayayyaki da babu ma'aikata a cikinsu guda 100, da kuma kera sabbin mutum-mutumin inji dubu 10. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China