Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bankin AIIB zai dukufa wajen inganta hadin gwiwa tsakanin bangarori da dama
2020-07-30 14:56:05        cri

An yi taron shekara-shekara karo na 5 na bankin zuba jarin samar da ababen more rayuwa na Asiya ko AIIB a takaice ta kafar bidiyo tsakanin ranakun 28 zuwa 29 ga wata. A yayin taron da aka yi a daren ranar 29 ga wata, an bayyana cewa, bankin zai ci gaba da aiwatar da tsarin hadin gwiwa tsakanin bangarori da dama, domin zaman abin koyi ta fuskar hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa.

Maryam Yang na dauke da karin bayani…

Barkewar cutar numfashi ta COVID-19 a bana, ta haddasa matukar illa ga tattalin arzikin kasa da kasa. Sabo da haka, bankin AIIB ya samar da dallar Amurka biliyan 10 domin ba da taimako ga kasashe mambobin bankin wajen dakile cutar COVID-19 da farfado da tattalin arzikinsu. Kuma bisa wannan shirin, ya zuwa yanzu, bankin ya riga ya samar wa kasashe guda 12 da suka hada da Indiya, Bangladesh da Thailand da sauransu taimakon kudi sama da dallar Amurka biliyan 5.9, domin taimakawa shirye-shiryen kasashensu. A taron da aka yi a daren ranar 29 ga wata, shugaban bankin AIIB Jin Liqun ya bayyana cewa, yadda ake fuskantar yaduwar cutar COVID-19 ya nuna rashin karfi na wasu kasashe, musamman ma a fannin kiwon lafiya da ba da jinya, a don haka, a nan gaba, bankin zai kara mai da hankali a wannan fanni. Ya ce, "A nan gaba, tabbas za mu raba wasu kudade don zuba jari kan ayyukan kiwon lafiya, a lokacin da muke raya ayyukan gina hanyoyi, da layukan dogo da tashoshin ruwa, ko kuma habaka ayyukan daidaita gurbacewar ruwa da sauransu. Sabo da aikin kiwon lafiya zai kyautata lafiyar al'umma, da kara karfin kasa wajen samar da kayayyaki. A don haka, zuba jari a wannan fanni na da matukar muhimmanci, kuma mun koyi muhimmin darasi daga wannan annoba."

Bankin AIIB wani sabon banki ne dake mai da hankali wajen raya bangarori da dama. Cikin shekaru 4 da suka gabata, bankin yana tsayawa tsayin daka kan ka'idojin yin musayar ra'ayoyi tsakanin bangarori daban daban kan yadda za a gudanar da ayyuka, da raba sakamakon da aka samu ga bangarori daban daban da abin ya shafa, lamarin da ya sa, ya kafa dangantaka mai kyau da sauran hukumomin sha'anin kudin kasa da kasa, wanda ya nuna ainihin ma'anar hadin gwiwar dake tsakanin bangarori da dama. Jin Liqun ya kara da cewa, akwai bukatar martaba ra'ayin hadin gwiwa tsakanin bangarori da dama a yayin da kasashen duniya suke yaki da cutar COVID-19. Ya ce, "Bayan yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, babu wata kasa da za ta iya cimma nasarar yaki da cutar ita kadai. Wannan shi ne dalilin da ya sa, bankin AIIB yake yin hadin gwiwa da bankin raya Asiya na ADB da bankin farfadowa da bunkasuwar kasashen Turai na EBRD, wajen samar da na'urorin jinya ga wasu kasashe, da zuba jari ga wasu kamfanoni masu zaman kansu, da kuma ba da taimakon kudi ga wasu gwamnatocin kasashe. Ko da yake, wasu na ganin cewa, dabarar ba ta da amfani, amma, a hakika dai, wannan shi ne hanyar da za mu iya bi domin warware matsalolin da muke gamuwa da su. Sabo da cikin watanni 4 ko 5 da suka gabata, idan babu goyon baya na tsarin hadin gwiwar dake tsakanin bangarori daban daban, ba a san yadda kasashen dake samun kudin shiga kadan za su iya fuskantar matsalolin da suka gamu da su ba."

Mambar tawagar ba da shawara ga bankin AIIB, tsohuwar ministar harkokin kudi ta kasar Nijeriya, kana, tsohuwar darektar gudanarwar bankin duniya Ngozi Okonjo-Iweala ta bayyana cewa, ya kamata bankin AIIB ya ci gaba da aiwatar da tsarin hadin gwiwar dake tsakanin bangarori da dama domin fuskantar sabbin kalubalolin da za a gamu da su a nan gaba. Tana mai cewa, "Ya kamata mu sake koyon tsarin hadin gwiwa tsakanin bangarori da dama, kamar yadda za a yi hadin gwiwa da kuma dukufa tare. Shi ya sa, bankin AIIB zai iya koyon darussa daga harkokin da suka faru a baya, domin raya tsarin hadin gwiwa tsakanin bangarori da dama yadda ya kamata. Sabo da tsarin na da muhimmiyar ma'ana, ya kuma taimaka musu, shi ya sa, ya kamata mu dawo kan tsarin."

An kafa bankin AIIB a hukumance a ranar 16 ga watan Janairu na shekarar 2016, bisa kiran kasar Sin. A halin yanzu, mambobin bankin ya karu daga guda 57 a farkon kafuwarsa zuwa guda 103, wadanda suka fito daga kasashen dake manyan nahiyoyi shida, kamar su nahiyar Asiya, da nahiyar Turai, da nahiyar Afirka, da nahiyar Amurka ta Arewa, da nahiyar kudancin Amurka, da kuma nahiyar Oceania. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China