Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AIIB ya amince da shigar Benin da Djibouti da Rwanda a matsayin mambobinsa
2019-07-14 15:44:04        cri

Bankin bunkasa kayayyakin more rayuwa a nahiyar Asiya wato (AIIB) ya amince da kasashen Benin, Djibouti da Rwanda don su zama mambobinsa, hakan ya sa a yanzu AIIB yana da mambobin kasashe 100.

Hukumar zartaswar AIIB ta amince da wannan matakin ne a lokacin taronta na shekara karo na 4 wanda ya gudana a birnin Luxembourg.

Kasashen uku wadanda ba sa daga cikin shiyyar, za su kasance a matsayin cikakkun mambobin AIIB ne bayan sun cika dukkan sharrudan zama mamba da kuma ajiye kason farko na kudaden da ake bukata a bankin.

Haka zalika, hukumar zartaswar AIIB ta zabi ministan kudin kasar Sin Liu Kun, a matsayin shugabanta.

Bisa la'akari da amincewar mambobin kasashe 100 a bankin, karfin adadin kudaden da aka amince da su zai karu zuwa dala biliyan 8.5, AIIB ya kasance wani muhimmin shirin raya ci gaba na gamayyar kasa da kasa, in ji Liu a lokacin taron bankin na shekara shekara.

Liu ya bayyana farin cikinsa bisa irin nasarorin da bankin AIIB ya cimma a cikin shekaru 3 da suka gabata, ya kara da cewa, AIIB ya samu wakilcin mai sanya ido na dindindin na babban taron MDD.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China