Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in MDD ya bukaci a taimakawa MINUSMA da kudade
2020-01-16 09:34:37        cri

Mataimakin babban sakataren MDD mai kula da ayyukan zaman lafiya Jean-Pierre Lacroix, ya yi kira da a kara samarwa dakarun majalisar dake aikin kiyaye zaman lafiya a kasar Mali (MINUSMA) kudade, a daidai gabar da ta kara wani aiki mai muhimmanci a yankin tsakiyar kasar.

Lacroix ya shaidawa kwamitin sulhu na majalisar cewa, a cikin watannin da suka gabata, tawagar MINUSMA ta yi kokarin aiwatar da mataki na biyu na aikin shimfida zaman lafiya da ta ke dauka a yankin tsakiyar kasar, yayin da ta ke ci gaba da ayyukanta da ta ke gudanarwa a yankin arewacin kasar.

Jami'in na MDD ya ce, tawagar ta mayar da hankali a yankin tsakiyar Mali ne, don kwashe muhimman kadarorinta, kamar na sama, da dakarun kai daukin gaggawa da na leken asiri, da sanya ido da kadarorin bincike daga Gao zuwa Mpoti.

Ya ce, zai yi wahala tawagar ta aiwatar da muhimmin aiki a tsakiyar kasar, idan har ba ta samu karin kudade ba. A baya ma, ta yi yunkurin yin haka, amma lamarin ya haifar gibi mai hadarin gaske a wasu yankunan arewacin kasar, inda ake mutakar bukatar kasancewarta.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China