Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya yi kira da a bar kasuwa ta yi halinta
2020-07-21 21:00:20        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci a kara kokari don ganin kasuwa ta yi halinta da ma bunkasa harkokin kasuwanci.

Shugaba Xi ya bayyana haka ne, Talatar nan yayin da ya shugabanci taron karawa juna sani tare da 'yan kasuwa.

Xi, wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban kwamitin kolin sojojin kasar, ya kara yin kira da a kara zage damtse, ta yadda sha'anin kasuwanci zai taka muhimmiyar rawa tare da samun gagarumin ci gaba. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China