Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi tir da shirin Amurka na hana 'yan JKS shiga kasar
2020-07-16 19:57:05        cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta yi tir da shirin da gwamnatin Amurka ke yi, na hana mambobin JKS da iyalan su shiga kasar, ma'aikatar ta ce daukar wannan mataki babban abun takaici ne.

Da take tsokaci game da hakan a yau Alhamis, yayin taron manema labarai na rana rana da aka saba gudanarwa a nan birnin Beijing, mai magana da yawun ma'aikatar Hua Chunying, ta ce a matsayin ta na kasa mafi karfi a duniya, idan Amurka ta aiwatar da wannan mataki, wace daraja ce za ta rage mata? Kuma wane misali za ta nunawa duniya idan ta aikata haka?

Hua ta kara da cewa, baya ga karya tsarin zamantakewar kasa da kasa, aiwatar da shirin na Amurka, zai kuma zubar da kimar ta a matsayin ta na kasa mafi karfi a duniya.

A jiya Laraba ne dai jaridar "The New York Times" ta wallafa cewa, gwamnatin shugaba Trump na shirin dakatar da 'yan JKS da iyalan su daga shiga Amurka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China