Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya yi rangadi a lardin Jilin na arewa maso gabashin Sin
2020-07-23 09:03:54        cri

Shugaban kasar Sin, kana babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya gudanar da ziyara a lardin Jilin dake arewa maso gabashin Sin.

Yayin ziyarar ta jiya Laraba, shugaban ya yi rangadi a gundumar Lishu ta birnin Siping, inda ya ganewa idanun sa yankin gwaji na wurin da ake sarrafa kayan lambu, da muhallin kungiyoyin manoma dake samar da nau'o'in hatsi, da wurin da ake kyautata amfani da bakar kasa, da ma wuraren da ake gudanar da noman zamani a manyan filaye. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China