Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta horar da 'yan sandan Somalia 200 domin inganta tsaro a kasar
2020-02-22 15:36:13        cri

Shirin wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afrika (AMISOM), ya bayyana a jiya cewa, ya horar da 'yan sandan Somalia 200, domin kiyaye doka da oda a jihar Hirshabelle dake yankin tsakiyar kasar.

Shirin na AU na aiwatar da tsarin mika ragamar tsaro, wanda a karkashinsa, zai rika mika ragamar tsaro ga jami'an tsaron kasar a hankali, tare kuma da janyewa daga kasar ya zuwa shekarar 2021.

A wani bangare na aikin shirin, 'yan sandan AMISOM na ci gaba da hada hannu da rundunar 'yan sandan Somalia, domin ba da horo da shawarar inganta kwarewarsu, ta yadda za su cimma matsayin ingancin aikin 'yan sanda na duniya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China