Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Somalia ta yi bikin cika shekaru 60 da samun 'yancin kai
2020-07-02 10:02:44        cri

Kasar Somalia ta yi bikin murnar cika shakaru 60 da samun 'yancin kai a ranar Laraba yayin da ake ci gaba da yin kiraye kirayen neman hada kai, duk da dinbin kalubalolin dake addabar kasar ta kahon Afrika.

Cikin sakonsa, shugaban kasar Mohamed Farmajo ya bayyana cewa, al'ummar kasar Somali za su ci gaba da sa himma da kwazo, duk da yanayin wahalhalun dake tinkarar kasar, kuma za su yin alfahari da muhimman ci gaba da suka samu.

Kasar Somalia ta samu 'yancin kai a ranar 1 ga watan Yulin shekarar 1960, tun daga wancan lokacin kasar ke gudanar da bukukuwan murnar samun 'yancin kai, a tsakan dare ana bikin daga tutar kasar sama a dukkan shiyyoyin kasar gami da babban birnin kasar Mogadishu.

A sakon taya murnar da ya gabatar, Francisco Madeira, shugaban tawagar jami'an shirin zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika a Somalia (AMISOM), ya ce, kasar ta shafe tsawon lokaci tana ci gaba da fafutukar kawo karshen tashin hankali a kasar, domin wanzar da zaman lafiya da bunkasa ci gaban Somalia, da nufin maido da kimar kasar a idanun sauran kasashen duniya da kuma shiga a dama da ita a harkokin kasa da kasa.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China