Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan bindiga sun hallaka mutane 10 a kauyen Kadunan Najeriya
2020-07-22 10:21:35        cri

Wasu 'yan bindiga sun hallaka mutane 10, ciki hadda dagacin kauyen Gora Gan dake karamar hukumar Zango-Kataf, ta arewacin jihar Kaduna a arewacin Najeriya.

Wata majiyar jami'an tsaro ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, cikin wadanda 'yan bindigar suka harbe yayin harin na yammacin ranar Litinin, hadda wani yaro mai shekaru 7, baya ga mutane da dama da aka jikkata.

Harin na wannan karo na zuwa ne, bayan da wasu 'yan bindigar na daban, suka kai hari kauyen Kukum Daji dake karkashin masarautar Kagoro ta karamar hukumar Kaura duka dai a jihar ta Kaduna. A wancan hari ma dai an hallaka mutane 21, tare da jikkata wasu da dama.

Mataimakin kungiyar kiristoci ta Najeriya reshen karamar hukumar Zango-Kataf Isaac Ango-Makama, ya tabbatar da aukuwar harin na baya bayan nan.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China