Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin mutuwar da aka samu a jihar Legos ta Najeriya sanadiyyar ruftawar gini ya kai 3
2020-07-12 16:38:59        cri

Yawan mutuwar da aka samu a sakamakon ruftawar gini a jihar Legas, cibiyar kasuwancin Najeriya, ya kai 3 ya zuwa ranar Asabar, yayin da hukumomin ayyukan ceto a kasar ke ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Ginin mai hawa uku ya rufta ne da safiyar ranar Asabar a lokacin da mazauna ginin ke barci dake titin Freeman, a yankin Legos Island.

Damilola Oke-Osanyintolu, shugaban hukumar ba da agajin gaggawa na jihar Legas, wanda ya tabbatar da sabbin alkaluman hasarar rayukan, ya ce, an kwashe gawarwakin mutanen da suka rasu zuwa dakunan aje gawa, yayin da wasu mutanen tara da suka samu raunuka suke karba agajin lafiya na gaggawa a cibiyar.

Oke-Osanyintolu ya ce, wadanda suka mutu sun hada da wani karamin yaro da kuma manyan mutane biyu, ya kara da cewa, hukumar agajin na ci gaba da binciko burabuzan ginin da ya rufta.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China