Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IOM za ta taimakawa Nijeriya rage barazanar COVID-19 a sansanonin 'yan gudun hijira
2020-07-18 17:25:33        cri

Hukumar kula da kaura ta duniya IOM, ta ce za ta tsawaita ayyukan shirinta na WASH, mai samar da ruwa da kayayyakin tsafar jiki da muhalli, domin rage barazanar yaduwar COVID-19 a sansanonin 'yan gudun hijira dake da cunkoson jama'a a yankin arewa maso gabashin Nijeriya dake fama da rikici.

Cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafinta, shugaban shirin WASH a Nijeriya Teshager Tefera, ya ce cutar COVID-19 na ci gaba da kawo tsaiko ga kiwon lafiya da rayuwar jama'a a kasar mafi yawan al'umma a Afrika.

Ya ce sabon shirin na IOM zai taimaka wajen kandagarki da dakile yaduwar cutar a yankuna 3 na jihar Borno, inda za a mayar da hankali kan 'yan gudun hijira da yankunan da suka fi fuskantar hadarin yaduwar cutar.

A cewarsa, ayyukan za su kai ga 'yan gudun hijira kimanin 420,000 a sansanoni 120 da wasu al'ummomi dake kusa da su, a birnin Maiduguri da garuruwan Konduga da Damasak na jihar Borno.

Karkashin shirin, za a samar da tsaftataccen ruwa, da kayayyakin kula da tsaftar jiki 22,000 dake kunshe da sabulu da bokiti da sauran wasu abubuwa ga mutanen dake cikin hadarin kamuwa da cutar.

A cewar hukumar dakile yaduwar cututtuka da kandagarkinsu ta Nijeriya, an samu sabbin mutane 595 da suka kamu da cutar a ranar Alhamis, wanda ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar a kasar zuwa 34,854, kuma daga ciki, an samu 593 a jihar Borno. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China