Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Nijeriya sun kashe shugaban 'yan bindiga tare da ceto mutane 32
2020-07-18 15:57:37        cri

Rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar da kashe wani shugaban kungiyar 'yan bindiga tare da ceto mutane 32 da aka sace, yayin wani samame a yankin tsakiyar kasar.

Kakakin rundunar sojin John Enenche ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, an kaddamar da samamen ne a ranar Litinin, a maboyar 'yan bindigar dake kauyen Tomayin na jihar Benue dake arewa maso tsakiyar kasar.

John Enenche ya ce an kashe Zwa Ikyegh, shugaban wata kungiyar 'yan bindiga a jihar Benue ne lokacin da sojojin ke farautar 'yan bindigar, inda wasu daga cikinsu suka tsere da raunukan harbi.

Ya kara da cewa, samamen ya kai ga ceto mutane 32 da 'yan bindigar suka sace, wadanda tuni aka hada su da iyalansu, ciki har da wadanda ake rike da su sama da wata guda. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China