Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin EU sun bayyana kwarin gwiwar cimma yarjejeniya yayin taronsu na jiya
2020-07-21 13:27:13        cri
Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel da shugaban Faransa, Emmnuel Macron da shugabar hukumar EU, Ursula von der Leyen, sun bayyana kwarin gwiwa game da cimma yarjejeniya, yayin da shugabannin Tarayyar Turai ke shiga yini na 4 na jerin tarukansu a Brussels, dangane da shirye-shiryen farfadowa bayan annobar COVID-19.

Da take isa majalisar tarayyar, Angela Merkel ta bayyanawa 'yan jarida cewa, an tsara wani shirin yarjejeniya bayan an shafe tsawon dare ana tattauanwa. Ta ce wannan wani matakin ci gaba ne dake bayyana fatan cimma yarjejeniya a ranar.

A nasa bangaren, Emmanuel Macron, ya yabawa ci gaban da aka samu kawo yanzu, yana mai cewa akwai yuwuwar cimma yarjejeniya biyo bayan takaddamar da aka sha. Shugaban na Faransa ya ce har yanzu abun da ake ja-in-ja a kai shi ne, jimillar abun da ake bukata na shirin da kuma yadda za a raba tallafi.

Ita kuwa Von der Leyen cewa ta yi, tattaunawar shugabannin ya shiga wani muhimmin gaba, kuma ta yi ammana cewa, shugabannin na Turai na neman mafita, kuma suna nuna kudurinsu na lalubo bakin zaren. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China