Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabar kwamitin EU: ya kamata a baiwa kowa allurar rigakafin annobar COVID-19
2020-05-20 10:31:03        cri
Shugabar kwamitin tarayyar Turai EU, Madam Ursula von der Leyen ta bayyana ta kafar bidiyo cewa, EU ta amshi kiran hukumar lafiya ta duniya WHO, wajen tattara kudade don tallafawa ayyukan binciken allurar rigakafin cutar mashako ta COVID-19, kuma kokarinta zai taimaka sosai ga ayyukan binciken. Ta jaddada cewa, da zarar an fitar da allurar rigakafi, ya zama tilas a tabbatar da cewa kowa da kowa zai samu damar amfani da ita.

Ta ce bai kamata allurar rigakafin COVID-19 ta zama wani abu mai daraja wanda zababbun mutane 'yan kalilan ne za su iya amfani da ita ba, ya kamata ta zama abu na kowa da kowa. Madam Ursula von der Leyen ta kara da cewa, ana bukatar zama tsintsiya madaurinki daya domin shawo kan wannan annoba. Yanzu lokaci ya yi na karfafa hadin kai tsakanin al'ummomin duk duniya baki daya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China