Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bukaci kasashen Afirka da su hada kai don samun alluran riga kafin COVID-19
2020-06-25 15:02:12        cri

Shugaban kasar Afirka ta kudu kana shugaban karba-karba na kungiyar tarayyar Afirka (AU) Cyril Ramaphosa, ya yi kira ga kasashen Afirka da su hada karfi da karfe wajen ganin sun samu alluran riga kafin cutar COVID-19 a kan lokaci.

Shugaban ya yi wannan kira ne yayin taron da aka shirya ta kafar bidiyo kan rawar da Afirka za ta taka wajen samarwa da cin gajiyar alluran riga kafin COVID-19.

Taron wanda ya hallara shugabannin Afirka da masana da sauran masu ruwa da tsaki, zai fito da wata taswira ce kan yadda za a bukaci kokarin 'yan nahiyar na samar da alluran riga kafi da zai yi aiki, mai sauki kana maras hadari.

Ya ce, abu ne mai muhimmanci a ce an samar da riga kafin a Afirka, yana mai cewa, muddin ana bukatar a gudanar da bincike tare da samar da alluran riga kafi da ba shi da wata illa ga daukacin al'ummar Afirka, wajibi ne dukkan kasashen nahiyar su hada kai.

Ramaphosa ya ce, ya kamata kamfanonin samar da magunguna na Afirka, su samar da wani bangare na riga kafin GAVI, ciki har da COVID-19 da shirin riga kafin cututtuka. A don haka, a cewarsa, akwai babban kalubale a gaban nahiyar dake bukatar kara zage damtse wajen gudanar da bincike, tantancewa da samar da irin wannan riga kafi. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China