Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IGAD ta yi tir da harin da aka kai harabar AU da MDD a Somalia
2019-10-15 10:33:05        cri

Kungiyar raya yankin gabashin Afrika IGAD, ta yi tir da harin da aka kai harabar ofishin shirin wanzar da zaman lafiya na AU wato AMISOM da ofishin MDD dake Mogadishu a ranar Lahadin da ta gabata, lamarin da ya yi sanadin raunata a kalla mutane 7, ciki har da jami'an AMISOM 3.

Sakataren zartaswa na kungiyar IGAD Mahboub Maalim, ya ce kungiyar na bayyana goyon bayanta ga wadannan hukumomin abokan hulda, wadanda ba za a iya misalta matukar muhimmancin ayyukansu ba.

Kungiyar Al Shabaab da tuni ta dauki nauyin harin ce ta harba makamin roka a sansanin Halane, wanda ya kasance mazaunin ofisoshin AMISOM da MDD da sauran hukumomin kasa da kasa dake hidimtawa al'ummar Somalia. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China