Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan wadanda suka kamu da COVID-19 a nahiyar Afrika ya haura 700,000
2020-07-20 10:04:09        cri
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka da kandagarkinsu ta nahiyar Afrika wato Africa CDC, ta ce zuwa safiyar jiya Lahadi, adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a fadin nahiyar ya kai 701,573.

Cikin rahotonta na baya-bayan nan da ta fitar a jiya, cibiyar ta ce adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a nahiyar ya karu daga 683,905 da yammacin ranar Asabar, zuwa 701,573 ya zuwa safiyar jiya Lahadi.

Cibiyar ta kara da cewa, adadin wadanda cutar ta yi sanadin rayukansu shi ma ya karu, zuwa 14,937.

Har ila yau, cibiyar ta Africa CDC, ta ce tuni mutane 369,120 daga cikin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar, suka warke.

Yayin da ake tsaka da fama da yaduwar cutar a fadin nahiyar, kasashen da ta fi shafa sun hada da Afrika ta kudu da Masar da Nijeriya da Ghana da Algeria da Morocco da kuma Kamaru. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China