Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan wadanda suka harbu da cutar COVID-19 a Afirka ya tasam ma dubu 450
2020-07-05 16:45:01        cri
Cibiyar dakile cutuka masu yaduwa dake nahiyar Afirka, ko kuma Africa CDC a takaice, ta sanar da alkaluman dake nuna cewa, zuwa ranar 4 ga wata, adadin wadanda suka harbu da cutar mashako ta COVID-19 a nahiyar ya kai 448,512, kana, yawan mamatan ya kai 10,903, kuma yawan wadanda suka warke daga cutar ya kai 216,195. Sakamakon tasirin cutar, Afirka na kara fuskantar matsalar rashin abinci.

Alkaluman kididdigar sun nuna cewa, yankin da cutar ta fi yiwa illa shi ne kudancin Afirka, sai kuma arewacin nahiyar.

Hukumar shirin abinci ta duniya ta fitar da wani rahoto kwanan baya, inda ta nuna cewa, duba da yadda annobar COVID-19 ke ci gaba da yaduwa a Afirka, gaba daya akwai mutane miliyan 57.5 a tsakiya gami da yammacin nahiyar, da miliyan 41.5 a gabashin nahiyar, wadanda zasu tunduma cikin matsanancin halin rashin abinci. Har wa yau, ruwan sama kamar da bakin kwarya, da mummunan bala'in ambaliyar ruwa da bala'in farin dango su ma zasu haifar da babbar barazana ga aikin samar da isasshen abinci a Afirka.

A kasar Senegal, annobar COVID-19 ta jawo tashin gwaron zabi na farashin abinci, ciki har da na shinkafa da gyada da kuma gero. Sakamakon rashin 'yan kwadago da kayayyaki, manoma da dama sun gaza wajen nomawa ko kuma sayar da amfanin gonansu.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China