Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump ya amince da taka rawa wajen hana wasu kasashe mu'amala da kamfanin Huawei
2020-07-15 20:59:56        cri

Shugaban Amurka Donald Trump, ya amince cewa yana da hannu wajen hana wasu kasashe yin duk wata alaka da kamfanin fasaha na Huawei na kasar Sin, muddin dai kasashen na son ci gaba da mu'amala da kasar Amurka.

Game da wannan barazana da shugaba Trump ke yiwa wasu kasashen duniya, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Hua Chunying, ta ce hakan ya kara tabbatar da cewa, kokarin hana kamfanin Huawei gudanar da harkokin sa, ba shi da alaka da wani batu na tsaron kasa, illa dai kawai wani batu ne mai nasaba da siyasa. Har ila yau, duniya na kara gane cewa, kasar Sin ba ta da aniyar muzgunawa, ko tsoratarwa, ko tunzurawa, ko danne wata kasa a duniya, kuma wadannan duka halaye ne na kasar Amurka.

Uwargida Hua ta yi wannan tsokaci ne yayin taron manema labarai na rana rana da aka saba gudanarwa, yau Laraba 15 ga wata a nan birnin Beijing.

Rahotanni dai na cewa shugaba Trump ya fada da bakin sa, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a fadar White House a jiya cewa, ya janyo ra'ayin wasu kasashe game da bukatar kauracewa amfani da kayayyakin fasaha da kamfanin Huawei ke samarwa, muddin dai suna son yin mu'amala da kasar sa. Har ma ya kara da cewa, kasashen da suka ki amincewa da wannan bukata, za su fuskanci matsala da Amurka.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China