Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta kakabawa wasu sassa da jami'an Amurka takunkumi game da batun jihar Xinjiang ta kasar
2020-07-13 19:32:27        cri

Kasar Sin ta kakabawa wasu sassa, da jami'an kasar Amurka su 4 takunkumi, biyowa bayan matakin da Amurka ta dauka, game da batun jihar Xinjiang ta kasar Sin.

A Litinin din nan ne dai gwamnatin kasar ta Sin ta bayyana kakaba takunkumin, ga 'yan majalissar dokokin Amurka da suka hada da Sanata Marco Rubio, da Sanata Ted Cruz, da dan majalissa Chris Smith, da Sam Brownback.

Da take tabbatar da hakan, uwargida Hua Chunying, ta ce matakin Amurka na tsoma baki cikin harkokin gidan kasar, ya yi matukar sabawa ka'idojin huldar kasa da kasa, ya kuma illata alakar dake tsakanin Sin da Amurka.

Hua ta ce batun jihar Xinjiang, harka ce da ta shafi cikin gidan kasar Sin, don haka Amurka ba ta da hurumi, ko wata dama ta tsoma baki a cikin sa. Har ila yau gwamnatin Sin a shirye take, ta kare ikon mulkin kai, da tsaro da ci gaba, da moriyar kasar ta. Za kuma ta kara azama wajen yaki da ayyukan ta'addanci, da 'yan aware, da masu tsattsauran ra'ayin addini.

A hannu guda kuma, tana adawa da duk wani mataki na tsoma baki cikin harkokin jihar Xinjiang, da ma sauran harkokin cikin gidan ta. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China