Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bukaci Amurka da ta gaggauta gyara kura-kuranta
2020-06-23 19:33:40        cri

Kasar Sin tana kira da babbar murya ga bangaren Amurka, da ya yi watsi da tunanin yakin cacar baki da ra'ayin nuna bambanci, ya kuma hanzarta dakatar tare da gyara irin wadannan ayyuka da ba su dace ba.

Mai magana da yawun ma'aikatar harakokin wajen kasar Sin Zhao Lijian wanda ya bayyana haka Talatar nan yayin taron manema labarai, ya ce, idan har Amurka ta gaza gyara kura-kuranta, to kasar Sin ba ta da zabi, illa daukar matakan da suka dace.

Zhao Lijian, ya yi nuni da cewa, wannan wani misali ne na yadda bangaren Amurka ke daukar matakan da ba su dace ba kan kafofin watsa labaran kasar Sin, matakin da ka iya kara shafar yadda kafofin watsa labaran kasar Sin suke gudanar da ayyukansu a kasar Amurka, da kara fito da munafunci kan batun 'yancin aikin jarida da fadin albakarcin baki da bangaren Amurka ke ikirari.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China