Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta nuna matukar rashin jin dadi game da dakatarwar da Birtaniya ta yiwa kamfanin Huawei
2020-07-15 21:22:52        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Sin Hua Chunying, ta bayyana matukar rashin jin dadin kasar Sin, game da dakatarwar da Birtaniya ta yiwa kamfanin Huawei daga aikin fasahar 5G da kamfanin ke aiwatarwa a kasar.

Hua Chunying ta yi wannan tsokaci ne a yau Laraba, yayin taron manema labarai na rana rana da aka saba gudanarwa a nan birnin Beijing. Ta ce Sin za ta dauki dukkanin matakai da suka dace, domin kare muradun ta.

Hua ta kara da cewa, Birtaniya ta dauki matakin siyasa kan harkar da ta shafi cinikayya da fasahar sadarwa, wanda hakan ke barazana ga hakkin Sinawa masu zuba jari a kasar.

Jami'ar ta kuma ce, Sin na dora matukar muhimmanci ga wannan al'amari. Kalaman na ta dai na zuwa ne, bayan da a jiya Talata, Birtaniyar ta ayyana dakatar da kamfanin Huawei na Sin, daga ci gaba da ayyukan samar da fasahar 5G da yake gudanarwa a Birtaniyar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China