Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ofishin jakadancin Sin yana tuntubar 'yan sandan Birtaniya domin tabbatar da asalin gawawwakin da aka gano cikin wata babbar mota
2019-10-28 19:39:15        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana a yau cewa, ofishin jakadancin kasar Sin dake Birtaniya yana tuntubar hukumar 'yan sandan kasar domin samun karin bayanan da abin ya shafa, dangane da gawawwaki 39 da aka gano a cikin wata babbar mota a jihar Essex ta Birtaniya a makon da ya gabata, ta yadda za a tabbatar da asalin kasashensu, amma kawo yanzu hukumar 'yan sandan Birtaniya ta bayyana cewa, ba a iya tabbatar da lamarin ba tukuna.

Yayin taron ganawa da manema labaran da aka shirya, jami'in ya yi nuni da cewa, masu safarar mutane ba bisa ka'ida ba babbar matsala ce da kasashen duniya ke fuskanta, ya kamata kasashen duniya su hada kai tare domin dakile matsalar, kasar Sin tana fatan hada kai da sauran kasashen duniya domin yaki da wannan barazana.

Geng Shuang ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan bangarorin da abin ya shafa, za su sanar da duniya hakikanin abubuwa, bai kamata ba su rika boye bayanai ko fadin abubuwa bisa son ransu, kana ya nuna cewa, ofishin jakadancin kasar Sin dake Vietnam shi ma yana tuntubar hukumomin da abin ya shafa na kasar domin samun karin bayanai.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China