Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Birtaniya za su tallafawa WHO don yakar cutar COVID-19
2020-03-24 11:48:19        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping da firaministan Birtaniya Boris Johnson, sun tattauna ta wayar tarho a daren Litinin, inda suka bayyana aniyarsu ta tallafawa ayyukan hukumar lafiya ta duniya (WHO) domin yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19, wacce ta zama ruwan dare ga duniya.

A madadin gwamnatin kasar Sin da al'ummar Sinawa, shugaba Xi ya mika sakon jajantawa ga gwamnatin Birtaniya da jama'ar kasar bisa yakin da kasar ke yi da annobar cutar COVID-19. Bisa bukatar da aka nema, kasar Sin ta gabatar da irin matakan da ta dauka na yin kandagarki da kuma dakile yaduwar cutar.

Xi ya jaddada cewa, kasar Sin tana fatan Birtaniya za ta yi aiki tare da bangaren kasar Sin domin samun nasarar takaita barazanar ci gaba da bazuwar annobar domin tabbatar da cudanyar al'umma da harkokin kasuwanci tsakanin sassan biyu.

Kasar Sin a shirye take ta bayar da tallafi ga kasar Birtaniya, shugaba Xi ya kara da cewa, yana da kwarin gwiwa kasar Birtaniya za ta samu galaba a kokarin da take na dakile yaduwar cutar COVID-19 karkashin jagorancin mista Johnson.

A nasaba bangaren, firaminista Johnson, ya taya gwamnatin kasar Sin da al'ummar Sinawa murnar nasarar da suka cimma wajen yin kandagarki da kuma dakile bazuwar cutar a kasar Sin bisa ga irin namijin kokari da kuma sadaukarwar da gwamnatin Sin da jama'ar kasar suka nuna.

Boris Johnson ya ce a halin yanzu, yanayin da ake ciki game da annobar COVID-19 a Birtaniya ya yi tsanani, ya kara da cewa, Birtaniya tana ci gaba da yin nazari da kuma koyon muhimman dabaru gami da fasahohin zamani da kasar Sin ta yi amfani da su wajen yin kandagarki da kuma dakile yaduwar cutar.

Firaministan ya ce, ya gamsu da kalaman shugaba Xi na cewa babu wata kasa a duniya da za ta iya tsame kanta daga cikin annobar, kuma ya kamata dukkan kasashen duniya su karfafa hadin gwiwarsu domin cimma nasarar kawar da cutar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China