Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Ya dace Birtaniya ta kaucewa tada tarzoma ta amince cewa yankin HK ya koma karkashin Sin
2020-06-03 20:24:15        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya shawarci Birtaniya da ta kaucewa tada tarzoma, ta kuma amince cewa yankin Hong Kong ya riga ya koma karkashin kasar Sin. Zhao Lijian wanda ya yi wannan tsokaci a yau, yayin taron manema labarai da ya gudana a birnin Beijing, ya ce tuni Sin ta cimma matsaya mai karko tsakanin ta da Birtaniya.

Jami'in ya kara da cewa, kamata ya yi Birtaniya ta yi watsi da salon tunani na cacar baka, da tunanin mulkin mallaka, ta kuma amince, da martaba cewa yankin Hong Kong ya riga ya koma karkashin kasar Sin, inda a yanzu yake matsayin yankin musamman na Sin.

Zhao Lijian ya jaddada cewa, sai an tabbatar da tsaron kasa ne kadai, za a kai ga aiwatar da manufar nan ta "kasa daya amma tsarin mulki biyu ". Kaza lika hakan ne kadai zai haifar ci gaba, da daidaito a yankin Hong Kong.

Daga nan sai Zhao ya bayyana dokar tsaron kasa mai nasaba da Hong Kong, a matsayin wadda za ta shafi wasu ayyuka 'yan kalilan, da matakai dake iya yin barazana ga tsaron kasar Sin baki daya. Kuma hakan ba zai yi wani tarnaki ga cin gashin kai na yankin Hong Kong ba.

Har ila yau, matakin ba zai raunata 'yancin al'ummar Hong Kong ba, da ma ikon masu zuba jari na kasashen ketare dake hada hada ta halal a yankin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China