Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwanaki uku a jere ba a samu sabon rahoton kamuwa da COVID-19 a birnin Beijing ba
2020-07-09 11:16:56        cri

Hukumar lafiyar birnin Beijing ta sanar da cewa, ba'a samu sabon rahoton kamuwa da cutar COVID-19 ba a ranar Laraba a birnin.

Wannan shi ya tabbatar da cewa, an shafe kwanaki uku a jere ba tare da samun sabon rahoton bullar cutar barkewar numfashi ta COVID-19 a babban birnin kasar Sin ba.

A rahoton da take fitarwa kullum, hukumar lafiyar ta ce, ba a samu sabon rahoton wadanda ake zaton sun kamu da cutar ba, sai dai an samu rahoton mutum guda dake dauke da cutar wanda bai bayyana alamomin cutar ba, kana an sallami mutane 32 daga asibiti bayan sun warke a ranar Laraba.

Daga ranar 11 ga watan Yuni zuwa 8 ga watan Yuli, an samu rahoton mutane 335 da aka tabbatar sun harbu da cutar a birnin, daga cikin adadin mutane 275 na ci gaba da karba magunguna a asibiti yayin da aka sallami mutne 60 bayan sun warke daga cutar. Akwai kuma wasu mutane 26 da ba su nuna alamomin kamuwa da cutar ba wadanda suke karkashin kulawar kwararrun masana kiwon lafiya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China