Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar harkokin wajen Sin ta bukaci Amurka ta daina tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar
2020-07-15 13:38:05        cri
A kwanan nan, Amurka ta yi biris da babbar adawar da kasar Sin ta nuna, har ta zartas da wata doka mai suna wai dokar 'yancin cin gashin kai ta Hong Kong. Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da wata sanarwa a yau Laraba, inda ta bukaci Amurka ta gyara kuskuren da ta yi, wato bai kamata ta aiwatar da irin wannan doka ba, har ma ya kamata ta dakatar da duk wani yunkurinta na yin shisshigi cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, ciki har da harkokin da suka shafi Hong Kong. Sanarwar ta kuma jaddada cewa, idan Amurka ta ci gaba da hakan, babu tantama kasar Sin za ta maida martani.

Sanarwar ta nanata cewa, dokar da Amurka ta zartas, ta bata sunan dokar kare tsaron kasa mai nasaba da yankin Kong Kong, da barazanar sanyawa kasar Sin takunkumi, abun da ya sabawa dokokin kasa da kasa da muhimman ka'idojin da suka shafi dangantakar dake tsakanin kasashe daban-daban. Gwamnatin kasar Sin ta nuna babbar adawa gami da la'antar irin wannan shisshigin da Amurka ta yi cikin harkokin gidanta.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China