Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masana kimiya a Najeriya sun kera na'urar gwajin COVID-19
2020-07-10 19:40:39        cri
Ministan kimiyya da fasaha na Najeriya, Ogbonnaya Onu, ya bayyana cewa, masana kimiyya a kasar sun kera wata na'urar gwajin cutar COVID-19 mai suna RNA Swift da za ta iya ba da sakamakon cutar nan take, cikin farashi mai sauki.

Ministan wanda ya bayyana haka jiya Alhamis ga manema labarai a Abuja, babban birnin kasar, ya ce, a 'yan watanni masu zuwa, za a yi amfani da nau' ar wajen gwada manoma miliyan biyar. Ana kuma fatan samar da na'uar guda miliyan 10 a karon farko.

A jawabinsa shugaban hukumar dake nazarin fasahohin da suka shafi kwayoyin halittu ta kasar Alex Akpa, ya ce na'urar da aka kera a kasar, za ta kara karfin Najeriya a fannin gwajin cutar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China