Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An canja lokacin bude makarantu a Najeriya
2020-07-09 19:54:08        cri
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa, ta canja lokacin bude makarantu a kasar, saboda yadda yawan masu kamuwa da cutar COVID-19 a kasar ya haura dubu 30 a halin yanzu.

Ministan Ilimi na Najeriya, Adamu Adamu, shi ne ya shaidawa manema labarai hakan jiya Laraba a Abuja, babban birnin kasar. Yana mai cewa, cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya, ta tabbatar da sabbin mutane 460 da suka kamu da cutar a daren jiya, adadin da ya kai mutane 30,249 da suka kamu da cutar a kasar ya zuwa wannan lokaci. Wannan adadi ya hada da mutane 684 da cutar ta kashe da mutane 12,373 da suka warke tun lokacin da cutar ta bulla a ranar 27 ga watan Fabrairu.

Ministan ya ce, karuwar wadanda suka harbu da cutar, ya damu gwamnatin Najeriya, abin da ya sanya ta yin tunanin cewa, shirin da aka yi a baya na bude makarantun kasar a ranar Litinin, ka iya zama mai hadarin gaske a wannan lokaci.

A don haka, ministan ya ce, saboda wannan shawara da aka yanke, dalibai ba za su shirya ko rubuta duk wata jarabawa ba, ciki har da jarabawar da hukumar shirya jarabawa ta yammacin Afirka (WAEC) ke shiryawa.

A ranar 29 ga watan Yunin wannan shekara ce, gwamnatin Najeriyar ta sanar da duba yiwuwar sake bude makarantun, don baiwa daliban dake shirin kammala karatunsu, damar komawa makaranta ta yadda za su kimtsa don rubuta jarabawa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China