Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi tir da harin da aka kai harabarta a Somalia
2019-10-14 13:31:54        cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi tir da harin roka da aka kai filin jirgin sama na kasa da kasa na birnin Mogadishu a jiya Lahadi, wanda kuma ya shafi harabar ofisoshin shirye-shiryen wanzar da zaman lafiya na majalisar da na Tarayyar Afrika wato AMISOM.

Harin da aka kai filin jirgin saman Aden Adde, ya jikkata mutane 6 a wurin da ofisoshin shiryen shiryen wanzar da zaman lafiya da ma ofisoshin jakadancin wasu kasashe suke.

Cikin wata sanarwa da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar, Antonio Guterres, ya yi wa wadanda harin ya rutsa da su fatan samun sauki cikin gaggawa.

Sanarwar ta kuma ruwaito Sakatare Janar din na jaddada goyon bayansa ga dukkan jami'an MDD dake Somalia, tare tabbatar da cewa majalisar, za ta ci gaba da goyon bayan gwamnatin da al'ummar Somalia a kokarin da suke na neman zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Tuni kungiyar al-Shabaab dake da alaka da kungiyar Al-Qaida, ta dauki nauyin kai harin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China