Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na neman yin hadin gwiwa da kasa da kasa kan nazarin cutar COVID-19
2020-07-09 09:44:02        cri

Kasar Sin ta shirya yin hadin gwiwa da kasa da kasa kan aikin nazarin bincike game da samar da magunguna, alluran rigakafi, kayayyakin gwaje gwaje, da kuma amfani da magungunan gargajiyar kasar Sin don yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

Ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar ce ta fitar da wasu muhimman bayanai a ranar Litinin, inda take neman a gudanar da wasu ayyukan hadin gwiwa da sauran kasashen duniya kimanin 37 game da cutar COVID-19 don mayar da hankali kan wasu ayyuka hudu. Manufar tsarin shi ne karfafa yin bincike na hadin gwiwa da kasashen duniya da dama da hukumomin kasa da kasa masu ruwa da tsaki ta hanyar yin kirkire kirkire na hadin gwiwa da kasa da kasa a fannin kimiyya da fasaha, da kuma yin musayar alkaluman bincike da kwarewar da aka samu wajen yaki da annobar.

Daga cikin ayyukan da Sin ta bukata sun hada da gwajin magani da alluran rigakafi, da yin hadin gwiwa don samar da sabbin fasahohin gwaje gwaje, da amfani da kayayyakin gwajin cutar cikin sauri, da kuma aikin nazari na kasa da kasa wajen jinyar masu fama da cutar COVID-19.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China