Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na tattaunawa da tsagin Amurka game da aniyar dakatar da zirga zirgar jiragenta da Amurka ke shirin yi
2020-06-04 19:21:16        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce hukumar dake lura da sufurin jiragen fasinja ta Sin ko CAAC a takaice, ta gabatarwa Amurka wakilci mai karfi, domin tattaunawa da sashen sufurin Amurkan, a gabar da Amurkar ke cewa za ta dakatar da zirga zirgar jiragen saman Sin.

Zhao Lijian, ya bayyana hakan ne a Alhamis din nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa. Tsokacin na sa, ya biyo bayan barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi a jiya Laraba, cewa tun daga ranar 16 ga watan nan, Amurka za ta hana jiragen saman Sin shiga ko fita daga Amurka.

Jami'in ya kara da cewa, hukumar CAAC ta jima tana tattaunawa da bangaren Amurka, game da tsara hanyoyin ci gaba da sufurin jiragen sama tsakanin kasashen biyu.

Kafin hakan, hukumar sufurin jiragen sama ta kasar Sin, ta fitar da wata sanarwa a yau, wadda ke cewa, za a ba da dama ga karin jiragen saman kasa da kasa, su rika zirga zirga zuwa cikin kasar. Hukumar ta ce ana daukar matakai ne gwargwadon yanayin da ake ciki, game da ikon dakile cutar COVID-19 a kasar ta Sin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China