Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta kaddamar da kwamiti mai zaman kansa da zai yi nazarin yadda aka tunkari COVID-19 a duniya
2020-07-10 10:29:18        cri
Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya sanar da kaddamar da wani kwamiti mai zaman kansa, da zai yi nazarci yadda duniya ta tunkari COVID-19 karkashin hukumar.

Da yake jawabi ga mambobin hukumar ta kafar bidiyo a jiya Alhamis, Tedros Ghebreyesus ya ce an kafa kwamitin ne karkashin tsohuwar firaministar kasar New Zealand, Helen Clark da tsohuwar shugabar kasar Liberia, Ellen Johnson Sirleaf, wadanda za su zabi mambobinsu.

Ana sa ran kwamitin ya miki kwarya-kwaryar sakamakon bincikensa a watan Nuwamba, lokacin da majalisar hukumar za ta dawo da zama, sannan ya bada cikakken rahoto a watan Mayun badi.

Ya ce wannan ba rahoto ne da za a ajiye ba, abu ne da za a dauka da muhimmanci. Yana mai cewa, ta hanyar kwamitin, duniya za ta fahimci ainihin abun da ya faru da kuma hanyoyin da za a kyauta makomar bil Adama.

WHO ta ce an kafa kwamitin ne bisa kudurin taron majalisarta da aka yi a watan Mayu, domin bitar darrusan da gogewar da aka samu da yadda kasashen duniya suka tunkari cutar COVID-19. Wannan rahoto ya shafi duniya baki daya, ciki har da rawar da hukumar WHO ta taka. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China