Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO:Yawan wadanda suka kamu da COVID-19 a duniya ya kai miliyan 10
2020-06-30 13:08:09        cri

Babban darektan hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana cewa, kasashen dake fama da cutar COVID-19, za su sake fuskatar cutar a watanni masu zuwa, yayin da a halin yanzu cutar ta harbi sama da mutane miliyan 10 a fadin duniya, ciki da kusan mutane dubu 500 da cutar ta halaka.

Darektan wanda ya bayyana haka yayin taron manema labarai jiya, ya ce babbar tambaya ita ce, yadda a cikin watanni masu zuwa, kasashen duniya za su kasance da wannan cuta. Wannan wani sabon abu ne. Ko da yake kasashe da dama sun samu nasara a kan wannan cuta, amma har yanzu cutar na ci gaba da yaduwa a duniya.

A don haka, ya bukaci kasashen duniya, da su mayar da hankali kan muhimman abubuwa guda biyar don kare rayukan jama'a, ciki har da samar da abubuwan yi ga al'ummomi da daidaikun jama'a ta yadda za su kare kansu da ma sauran jama'a, rage yaduwar cutar, ceton rayuka ta hanyar amfani da iskar Oxygen da dexamethasone ga misali, hanzarta gudanar da bincike kan COVID-19 da karfafa shugabanci na siyasa da sadaukar da kai.

Bugu da kari, Tedros ya sanar da ci gaban da aka samu da ma wa'adin da WHO ta ayyana kan matakan yaki da cutar, ta yadda jama'a za su fahimci yadda hukumar take daukar matakan yaki da wannan annoba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China